Shugaban hukumar ‘yan sanda na ƙasa, Mohammed Adamu ya ba da umarnin hana zirga-zirgar ababen hawa daga ƙarfe 11:59 na safiyar Juma’a zuwa 6.00 na safiyar Asabar, a Jihar Edo, inda za a yi zaɓen gwamna a ranar Asabar.
Mohammed Adamu ya ce rundunarsa ba za ta lamunci tashin hankali ko satar akwati ko kasuwancin ƙuri’u ko kalaman nuna tsana ko duk wani abin da zai yi tasgaro ga zaɓen ba.
“Hana zirga-zirgar za ta daƙile shige da fice da kuma yaɗuwa ko amfani da haramtattun makamai da ƙwayoyi tare da hana kai-komon ’yan bangar siyasa da sauran miyagu musamman daga jihohin maƙwabta da ke iya lalata tsarin zaɓen”, inji sanarwar rundunar.
Sanarwar da kakakin rundunar, DCP Frank Mba ya fitar ta ce ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun yi cikakken shiri domin tabbatar da ganin zaɓen ya gudana cikin lumana da tsafta.
Ya buƙaci jama’ar jihar Edo da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin bin doka ba tare da fargaba ba, sannan su yi tururuwa wajen jada ƙuri’unsu.