Zaɓen Osun, sai yafi na Ekiti Inganci — Alwashin Shugaban INEC ga Masu Kaɗa ƙuri’a
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bada tabbacin cewa zaɓen Gwamnan Jihar Osun na 16 ga watan Juli na Shekarar 2022, zai fi inganci, musamman akan abubuwan da suka shafi kuɗaɗe fiye da na Zaɓen Ekiti da aka gudanar a satin daya gabata.
Farfesa Yakubu ya bada wannan tabbacin a ranar Asabar a Abuja.
A taron na gangamin wayar wa Matasa kai kan Zabe, ya gudana a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadimar Buhari Onochie, ta musanta batun cewa Tinubu bai da Takardun makaranta
Ya buƙaci Matasa dasu cigaba da nuna sha’awa wajen shiga harkokin zaɓe, musamman yin Katin Zaɓe, yana mai cewa zasu cigaba da rajistar katin zaɓe.
Yace “Matasa zasu so suji yaushe ne rajistar katin zaɓe zata ƙare..ina mai baku tabbacin cewa madadin Hukumar, ba zamu tsaida rajista a ranar 30 ga watan Yuni ba, idan dai har kuna yin rajista, zamu cigaba da yi maku. A cikin kwanaki biyar, mun yiwa sama da ƴan Najeriya dubu 14,000 rajista a wannan wurin da muke, muna da na’urorin rajista sama da guda 50.
“Zuwa ranar Litinin zamu ƙaro wasu Na’urori. Ba zamu daina rajista ba, har sai mun gamsu cewa mun ba kowa dama domin yayi rajista.
“Zaɓen Gwamnan jihar Osun zaifi inganci akan na Ekiti, sannan na 2023 zaifi kowane inganci. Zamu kirga ƙuri’un ku. Ga waɗanda basu yi rajista ba, suje suyi.