A ranar Lahadi 9 ga watan Janairu Jam’iyyar APC zata yi taro domin fitar da ranar da za’ayi zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa.
Wannan wani martani ne akan abinda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya faɗa a tattaunawar da gidan talabijin na NTA ya watsa a ranar Alhamis.
A tattaunawar, Buhari ya gargaɗin cewa, rashin shiri da wuri, Jam’iyyar APC ta shirya shan kaye daga abokiyar hamayyar ta Jam’iyyar PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kashe ‘Yan Ta’adda 950 Da Suka Hadar Da Kwamandoji da Sarakunansu -Shedikwatar Tsaro
Shugaban Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jahar Filato Simon Lalong Wanda ya yi taro da Shugaban Ƙasa a ranar Juma’a a Abuja, yace gargaɗin Buhari, wani ƙarin ƙwarin gwuiwa ne ga Jam’iyyar ta yi taron, domin gudun shan kaye.
Lalong yayi jawabin ne da ƴan jarida a Villa, inda yace taron ranar Lahadi, zai fito da ranar da za’a gudanar da zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa.
Yace Gwamnonin APC sun bada tabbacin su ga Shugaban Ƙasa cewa, zaɓen zai gudana a watan Fabrairu.
A cewar su Jam’iyyar zata rubanya ƙwazon ta, domin tayi abinda ya dace.
Gwamnan Jahar Filato yace duk da an zargi jam’iyya da ɓata lokaci, amma koma minene a ƙarshe dai zata zaɓi Shuwagabannin ta.
Gwamnan ya bayyana cewar, duk da irin damuwar da Shugaban Ƙasa ya nuna, Gwamnonin a shirye suke, kuma babu abinda zai hana su gudanar da zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar cikin kwanciyar hankali.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin yace suna ɗaukar dukkanin matakai domin magance dukkanin matsalolin da zasu hana zaɓen Shuwagabannin na ƙasa.