Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai goyi bayan duk wani matashi a duk wani mukami a zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar APC na Ƙasa.
Shugaban Ƙasar wanda ya baiwa Shugaban Ma’aikata Ibrahim Gambari da Sakataren Gwamnatin Jaha Boss Mustapha daya tabbatar dukkanin Ma’aikatu da Shuwagabannin Hukumomi dasu tabbatar da cewa Matasan dake da jajircewa an sanya su a Kwamitoci na Gwamnatin Tarayya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Jikkata Mutane 5 A Abuja
Buhari ya bada umarnin a lokacin da ya karɓi mambobin Ƙungiyar Matasa ta National Youth Lobby Group a Abuja.
Buhari ya kuma amince da kafa kwamitin Shugaban Ƙasa akan Matasa tare da Shugaba Matashi, yana mai kira ga Mustapha da Gambari da yayi aiki domin fito da hanyoyi domin tabbatar dashi.
“Zan goyi bayan tunanin matasa wanda suke neman matsayi a zaben Shuwagabannin Jam’iyya mai zuwa,” inji shi.