Jagoran ƴan adawar Uganda Bobi Wine ya ce bai yarda da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ranar Alhamis ba, kana yana fargabar halin da zai iya faɗawa tun bayan da sojoji suka kewaye gidansa.
Ya shaida wa BBC cewa ɗaruruwan sojoji sun tare a gidansa tare da iyalinsa, baya ga cin zarafin wasu magoya bayansa da suka riƙa yi.
Ranar Asabar ne hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen a hukumance, inda ta bayyana shugaba mai ci Yoweri Museveni a matsayin wanda ya samu nasara da tazara mai yawa.
Bobi Wine da sauran ƴan takara goma da suka shiga zaɓen sun yi zargin tafka maguɗi, da kuma hana wakilansu sanya ido.