Rahotanni na nuni da cewa; kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta Kara da Liverpool a Ranar 29 ga watan Agusta nan da muke ciki a gasar wasan karshe na Community shield.
Rabon da kungiyoyi biyun nan su hadu a gasar Community shield tun a shekarar 2002 wasan da Arsenal take doke Liverpool daci 1-0 ta hannun Dan wasa Gilberto a minti na 69.