Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce za a bude masallatai ranar Litinin a a biranen da cutar korona ba ta bazu sosai ba.
Shugaban ya ce za a dawo da yin sallar Juma’a amma sai idan masallatan sun kiyaye matakan kariya.
Ya kara da cewa za a ci gaba da bude harakokin kasuwanci, yayin da tuni aka ba masu aski da cibiyoyin wasanni damar budewa.
Cutar korona ta fi yi wa Iran illa a yankin Gabas ta tsakiya, inda alkalumma suka nuna sama da mutum dubu shida suka mutu, ko da yake ana ganin alkalumman sun fi haka. Inji rahoton Bbc.