Hukumar daƙile cuttuka masu yaɗuwa ta ƙasar China, ta hannun Guizhen Wu ta bayyana cewa ta samar da maganin annobar Korona, kuma ta sa ran a farkon makon watan Nuwamba za a fara sakinsa ga kowa da kowa.
Gidan Talabijin na France24 ta rawaito cewa ƙasar China ta haɗa aƙalla magungunan Korona har kala huɗu, kuma guda uku daga ciki suna matakin ƙarshe, a yanzu haka an fara yin gwajinsu domin tabbatar da sahihancinsu.
Wu ta bayyana cewa magungunan guda uku an kammala haɗa su, suna matakin ƙarshe na gwaji kuma ana sa ran a cikin watan Nuwamba ko Disamba za a fara sakinsu a kasuwa.
https://dimokuradiyya.com.ng/yaƙi-da-cutar-korona-a-nahiyar-afirka-na-yin-kwan-gaba-kwan-baya/
Wu ta ƙara da cewa a watan Afrilu an mata gwajin ɗaya daga cikin magungunan kuma har yanzu garau take jin kanta babu wani nau’in ciwo dake damunt.
Sai dai ya zuwa yanzu babu wani sahihin maganin annobar ta Korona da za a iya cewa ana amfani da shi, amma dai masana da dama sun ci gaba da bincike domin samun maganin annobar.