An sanya ranar da za a fara gasar share fage ta gwamnan jahar Rivers wato gwamna Wike karo na biyu bayan da akayi gasar a shekarun baya inda a aannan lokacin za ayi gasar karo na biyu wato a watan gobe na Nuwamba.
Wannan sanarwar ta cewa za a fara wannan gasa da gwamnan na Rivers zai ɗauki nauyi ta fito ne daga bakin mai shirya gasar a madadin gwamnan wato Badawiy Bashir wanda ya sanarwa da masu manema labarai.
Za a fara gasar daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa ranar 10 ga wata inda za a kwashe kwanaki 10 ana gudanar da gasar kenan. A karon farko da akayi gasar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sunshine Stars na garin Akure ne suka zamo zakara.
The Kwara United General Manager stated further that arrival date for all teams will be Friday 30th October with accreditation and draws taking place a day later.
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan fa zasu fafata wannan gasar ta share fage sune Lobi Stars da Abia Warriors da Plateau United da Kwara United da Bendel Insurance da Rivers United.
Ragowar ƙungiyiyin ƙwallon ƙafan akwai Gombe United da Remo Stars da Niger Tornadoes da Nasarawa United da kuma Cynosure FC.
General Manager na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kwara United wanda yana cikin ‘yan kwamatin shirya wannan gasa ya bayana cewar dukkanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da zasu fafata wannan gasa zasu kasance a jahar ta Rivers a ranar 30 ga watannan na Oktoba.
Sannan kuma dukkanin wasannin za a dinga fafatasu a filin wasa na Sharks dake Port Harcourt wanda filin wasa ne wanda yayi shuhura sosai a ƙasar Najeriya.