Majalisar jihar Kano, ta sanya hannu a wata doka wacce za ta bai wa sabuwar Kwalejin karantar da Unguwanzoma a mataki karamar Diploma da kuma babbar Diploma da kuma digiri.
Da yake karanta dokar a ranar Litininn, shugaban mafiya rinjaye, Alhaji Labaran Abdul-Madari ya ce; Kwalejin wacce a da ake karatu zuwa mataki Satifiket kawai, a bunkasa ta yanzu ta yadda za ta rika karantarwa har zuwa mataki digiri.
A cewarsa, dokar za ta kuma bai wa Kwalejin damar bai wa dalibai dama wadanda suka samu darussa 5 a matakin Sakandare wanda ya hada da darasin Mathematics, English da Biology musamman wadanda suka fito daga yankunan karkara domin samun horon shekara guda akan abin da ya shafi ilimin Unguwanzoma da kuma lura da lafiya.
Ya tabbatar da cewa za a fi bai wa wadanda suke karkara muhimmanci domin ganin an ilmantar da su ilimin lura da lafiya, wanda ya ce hakan zai taimaka wajen rage adadin da suke rasa rayukansu a yayin haihuwa a karkarar.
Ya tabbatar da cewa wadanda suka kammala makarantar, kananan hukumomi za su ba su aiki domin bunkasa bangaren kiwon lafiya a yankin.