Iyaye da Kungiyoyin Kiristoci a Ghana sun yi watsi da batun shirye-shiryen fara koyar da ilimin jima’i ga yara ‘yan shekaru hudu a makarantun firamare.
Bbc Hausa sun labarto cewa; masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi a kasar sun bayyana cewa hukumar UNESCO wato Hukumar Ilimi da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya za ta taimaka wa yara da bayanai kan ilimin jima’i da kuma matsalolin da ake fuskanta.
Daraktan Ilimi na Ghana ya bayyana cewa irin wannan ilimin zai taimaka wajen ”kara gyara tarbiyyar yara, da sanin ya kamata da ganin girman juna da kuma sanin abin da ya kamata dangane da ko wane jinsi.”
Sai dai kungiyoyi a Ghana na ganin wannan tamkar makarkashiya ce da za a bi wajen koya wa yara luwadi da madigo.
Shugaban wata kungiya da ke yaki da luwadi da madigo ta ”National Coalition for Proper Human Sexual Rights and Family Values” wato Moses Foh Amoaning ya shaida cewa ”Wannan wani shiri ne kawai a boye da ba za su fito fili su bayyana ba.”
Iyaye da Kungiyoyin Kiristoci a kasar na ci gaba da saka alamar tambaya kan dalilin da zai sa a fara koyar da yara ilimin jima’i a makarantun firamare tun kafin su balaga, inda iyayen suka bayyana haka a matsayin shedanci.
Za a fara koyar da ilimin bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi a wannan sabon zangon karatun na 2019.