Hukumar Kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta Ƙaddamar da taron wuni hudu na masu ruwa da tsaki a fannin inganta lafiyar al’umma kan yadda za a sami nasarar aiwatar da sabon tsarin inganta lafiya a dukkanin matakai wato Minimum Service Package.
A jawabinsa yayin bude taron, Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano Dr. Tijjani Hussaini yace, an shirya taron ne domin duba sakamakon da aka cimma a shekarar data gabata domin samar da tsarin gudanar da ayyukan duba lafiyar al’umma a awa ashirin da hudu a wasu daga cikin asibitocin da aka zaba a karkashin shirin na sabon tsarin inganta lafiya wato MSP.
Dr. Hussein ya kara da cewar tsarin bazai samu Nasara ba har sai dukkanin masu ruwa da tsaki sun bada gudunmawar su wajen samun nasarar tsarin.
Daga nan ne sai ya nemi hadin kan dukkanin Daraktocin Shiyya da shugabannin kula da bangaren lafiya a kananan hukumomi dasu marawa yunkurin baya domin samun nasarar aiwatar da shirin kula da lafiya na awa 24 a kananan hukumomin nasu.
Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Maikudi Muhammad Marafa cikin wata Sanarwa da ya aikowa da Dimokuraɗiyya ya ce Muhimman batutuwan da aka duba sun haɗar da yadda za a samar da sabbin gine-gine, da inganta harkar ma’aikata da Kuma samar da magunguna a cibiyoyin Kula da lafiya a karkashin sabon tsarin Kula da lafiya wato MSP.