Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce za ta fara jigilar maniyyatan jihar a yau Lahadi, bayan da maniyya daga jihohin kasar nan dama kawo yanzu suka isa kasar Saudiyya.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar Yusuf Abdullahi ya fitar yau Lahadi.
KU KARANTA: Otti Ya Umurci Jami’an Gwamnatin Data Shude Su Maido Da Kadarorin Gwamnati
Sanarwar tace za a fara da Maniyyatan kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada da Bebeji da Garun Malam.
Haka kuma an umarce su da su fita sassanin alhazai na Kano a yau da karfe 8 na daren domin tafiya Kasa Mai tsarki.
Haka kuma sanarwar ta yi kira ga maniyyatan da su fito sanye da kayan da aka basu na bai daya, domin dai aikin ya tafi cikin tsari.
A wani labarin kuma: Cire Tallafin Fetur: Kuyiwa Allah Kada Ku Tafi Yajin Aiki, Ndume Ya Roki NLC
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya roki shugabannin NLC da kada su tafi yajin aiki.
Ndume ya roki shugabannin kungiyar NLC da su shiga tattaunawa a matsayin wata hanya ta daidaita lamarin.
Ndume yayi kira ga shugaban kasa Tinubu, da ya gana da shugabannin kungiyar kwadago da kan sa.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, APC, Borno ta Kudu, ya roki shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC da su janye yajin aikin da ake sa ran za a fara ranar Laraba mai zuwa.