Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ce yana wasu tsare-tsaren soma yi wa duk mutumin da zai shiga jihar gwajin cutar korona.
Gwmanan ya shaida hakan ne lokacin da yake ƙarban bayanai daga kwamitin da ke yaƙi da annobar a Jihar, ya kuma kara da cewa zai yi aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an bi dokoki kare kai daga kamuwa da cutar a jihar, a cewar jaridar Today.
Jaridar ta kuma ambato gwamnan na cewa duk wani mutum da zai shiga jihar dole a yi masa gwaji, a wani mataki na takaita yaduwar annobar.
Sannan ya shaida cewa za su yi aiki tare da sarakuna da malaman addini da na jami’o’i da makarantu domin aike sakonni bin dokokin kariya.
Daga watan Disamba shekarar da ta gabata zuwa 19 ga watan Janairu 2021, annobar ta kashe mutane 17 a Kano, mutum 71 kuma tun bullarta a ranar 11 ga watan Afrilun 2020.
Mutane 827 cutar ta kama cikinsu kuma akwai 289 da har yanzu ke kwance a asibiti kamar yadda BBC Hausa ta labarto.