Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin fara yiwa masu maƙaman gwamnati, ma’aikata da kuma ɗalibai masu neman shiga makarantun gaba da Sakandare gwajin ƙwaya.
Wannan na ɗauke ne a cikin wata takarda da Kwamishinan yada labarai Malam Muhammed Garba ya fitar, inda ya bayyana cewa gwamnatin zata fara yin gwajin ne da zarar hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta jihar Kano ta gamawa shiryawa tsaf domin yin gwajin.
Gwamnatin Ganduje ta nuna sha’awarts wajen yaƙi da shan miyagun kwayoyi a jihar Kano kamar yadda ta dinga shirya taruka daban-daban.
Gwamnan ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da zan hankali a kafafen sada zumunta akan yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi.
Idan ba a manta ba majalisar dinkin duniya ta ware ranar 26 ga kowanne watan Yuli shekara a matsayin ranar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi.