Rahotanni sun bayyana cewa kafin daren yau ne za a gurfanar da masu zanga zanga a Lekki Toll Gate.
Femi Falana, wani babban lauyan Nigeria, ya shaidawa jaridar TheCable a ranar Asabar cewa, wadanda aka cafke a yayin zanga zangar za su gurfana gaban kotun tafi da gidanka a Yaba, Lagos.
A cewar Falana, a halin yanzu an tsare su ne a sashen binciken ta’addanci na rundunar ‘yan sanda da ke Panti.
Wadanda ake zargin sun mamaye Lekki a ranar Asabar a wata zanga zanga da suke gudanarwa, ta nuna rashin amincewa da wani umurni da aka baiwa kamfanin Lekki Concession da ya dawo ya ci gaba da karbar haraji a gadar.
Masu zanga zanga da yawa, ciki kuwa har da Mr Macaroni, wani mai wasan barkwanci, sun shiga hannun jami’an tsaro a babbar gadar.
Wasu ma da suka yi ikirarun su masu sa ido ne, an yi awon gaba da su.
Wani kwamitin shari’a da gwamnatin jihar Lagos ta kafa domin yin bincike kan tauye hakkin bil Adama da aka yi a ranar 20 ga watan Oktoba 2020, tare da harbe harbe a gadar Lekki, ya amince kamfanin LCC ya dawo ya ci gaba da karbar haraji a gadar.
Falana wanda ya kasance shugaban tafiyar ASCAB kan COVID-19 da sauran cututtuka (ASCAB), ya kuma bukaci da rundunar ‘yan sanda ta gaggauta sakin wadanda ta cafke a bakin gadar Lekki, a jihar Lagos.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Falana ya ce ASCAB ta tabbatar da cafke sama da matasa 20 wadanda suke da niyyar shiga cikin wannan zanga zangar lumanar a gadar.
Ya ce an karya dokar ‘yancin dan Adam, don haka ya zama wajibi a saki wadanda aka kama.