Kasa da kwana biyu da raba sama da naira miliyan 60 a matsayin bashin siyan gida da wadansu Malamai da ma’aikata da gwamnatin jihar Ekiti ta yi, gwamnatin ta sake raba naira miliyan 100 a matsayin bashin siyan mota ga ma’aikata 278.
Akintunde Oyebode, Kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arzikin jihar, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata a Ado Ekiti.
Da yake bayani kan yadda aka raba bashin, ya ce an raba ne daga naira dubu tamanin zuwa naira miliyan daya da dubu dari biyar bisa lura da matakin aikin mutum.