Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa za ta sanya Almajirai dubu daya da dari uku da ashirin da biyu a makarantun boko bayan wasu jihohin sun taso keyarsu zuwa gida sakamakon cutar annobar Korona.
Gwamna Badaru na jihar ne ya sanar da hakan a yayin zantawa da manema labarai a Dutse game da halin da jihar ke ciki kan annobar.
A cewar gwamnan, ya bada umarnin yi wa Almajiran rijista a makarantun firamare don fara karatun boko, sannan kuma za su ci gaba da karatun Al-Kur’ani.
Almajiran da aka maido da su gida daga wasu jihohin gwamnan a kwanakin baya ya ce suna samun kyakkyawar kulawa, yayin da ya ce, 23 daga cikinsu da aka samu dauke da cutar Korona, yanzu haka suna ci gaba da karbar magani a cibiyar da ake ci gaba da killace su. Inda kuma ya ce tuni aka mikawa Iyayen sauran almajiran.