Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka kama da cin zarafin mata. Hakan ya biyo bayan kiraye-kiraye da korafi da aka dinga a kafofin sadarwa dangane da irin cin zarafi da fyade da ake yi wa manya da kananan mata.
Hakan ya fito daga bakin Muhammadu Buhari a lokacin da yake yiwa ‘yan kasa jawabi a yayin bikin murnar ranar Dimokradiyya a jiya, a Abuja.
Shugaba Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa da irin yadda mata suke fuskantar cin mutunci daga wasu bata gari wanda basu san darajar mata ba.
Buhari yayi alkawarin yin aiki da ‘yan jarida, wajen ganin an wayar da kan al’umma muhimmanci mata da irin rawar da suke takawa a rayuwarmu ta yau da kullum.
Buhari ya jadadda goyon bayansa ga mata, duba da irin halin da suka tsinci kansu a kasar nan, ya kuma basu tabbacin kariya ga duk wanda aka kama ya keta haddin wata.