Al’ummar jihar Adamawa na iƙirarin maka tsohon gwamnan jihar Muhammad Umar Jibrilla (Bindow) a kotu idan bai tsayawa takara ba a zaben 2023, inda suka ce sun ɗanɗana kuɗar su.
Magoya bayansa a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa, Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu, da Maiha ne suka bayyana hakan a yayin wata ziyarar goyon baya da suka kai masa a gidansa da ke Yola da Mubi. Sun sha alwashin gurfanar da tsohon Gwamnan a gaban kotu idan bai tsaya takara a zaben 2023 mai zuwa ba.
Wata kungiya ƙarƙashin jagorancin Abubakar Ahmed Marafa a Yola, ita a fara umartan tsohon Gwamnan da ya sake tsayawa takara takarar kujerar gwamnan jihar a 2023 tare da gargadinsa da cewa idan bai yi ba za su haɗu a kotu.
Mai magana da yawun tawagar Abubakar Musa Adda, ya ce ya kamata tun yanzu Bindow ya ƙudiri aniyar sake tsayawa takara saboda al’ummar jihar na kewan gwamnatin sa.
Musa ya ce “Ranka ya daɗe, abin da muke faɗa maka ba ƙira bane domin baya neman ka yi shawara, ko baka da niyya sai mun tara maka kuɗi ka sake tsayawa takara kuma idan ka ce a’a kotu ce za ta raba mu.”
Yayinda yake a Mubi, mahaifarsa, ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC, Alhaji Jalo Mohammed daga ƙaramar hukumar Maiha ya jagoranci manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar inda a nan ma ya jaddada masa cewa babban laifi ne zai aikata idan ya ƙi amincewa ya sake tsayawa takara.
Ko dayake ya yarda cewa mutanen Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu, da Maiha sun tafka babban kuskure a zaben 2019, Alhaji Jalo ya nemi afuwan gwamnan da ya gafarta masu laifukan da suka yi saboda sun yi danasanin juya masa baya da suka yi.
“Ba za mu sake maimaita irin kuskuren da muka yi a baya ba saboda mun koyi darussan da dama domin mun ɗanɗana kuɗar mu”. Inji Jalo, makar yadda majiyar mu ta TG News ta ruwaito.
A nasa martanin, tsohon Gwamnan Muhammad Bindow Jibrillah ya ce lokaci bai yi ba da za a fara siyasa kuma ziyarar tasa ba ta da nasaba da manufar siyasa, ya zo ne domin jajantawa da yawa daga cikin ƴan uwa da abokan siyasa bisa rashe-rashen da aka yi a lokacin da baya nan.
Ya yaba da dubban mutanen da suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatan su don yi masa maraba.
Ya yi kira gare su da su tabbatar sun yi rijistar katin shaidar zama ƴan jam’iyar APC da za a fara a kwananan tare da sabunta rijistar ga waɗanda suka riga da suka yi a baya.
-Hausa Daily Times