Rahotannin da ke shigo mana na nuni da cewa; za a gabatar da jerin gwanon gawarwakin tsoffin shugabannin Masar 22 a birnin Alkahira a yau Asabar, inda a taron za a sauya su zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi da ke kudancin birnin kasar.
Bayanai sun nuna cewa ana sa ran cincirindon jama’a za su yi jerin gwano kan tituna domin kallo inda za su ga sarakuna 18 da sarakuna mata huɗu na Masar da za a ɗauka cikin akwatin zinari.
Za a jera su ne a tsarin tarihin mulkinsu yadda suka gudanar a tarihin da ya gabata.
Sai dai an ce za a tsaurara matakan tsaro, musamman ma duba da yadda ɗaukarsu da ake a matsayin masu daraja kuma matsayin dukiyar ƙasa.
Sarakunan sun ƙunshi har da Sarauniya Hatshepsut ta biyar a Masar da Fir’auna da ake kira Ramses na biyu.