A halin yanzun, Likitocin Asibiti sun gamsu da ana iya sallaman Jariri mafi kankanta a lokacin haihuwa a duk Duniyar nan, domin uwarsa ta dauke shi zuwa gida. Jaririn wanda aka haife shi a watan Oktoba, a wani Asibiti da ke kasar Japan, jaririn wanda nauyin shi bai daran ma nauyin kwaran Apple daya ba a lokacin da aka haife shi. Jaririn da aka sanyawa suna da, Ryusuke Sekiya, an haife shi bayan da ya kwashe makwanni 24 da kwanaki biyar kacal a cikin mahaifiyarsa mai suna, Toshiko, wacce ke fama da matsalar hawan jini. Gram 258, shi ne nauyinsa a lokacin haihuwar na shi, wanda hakan ke nufin ya gaza nauyin Jariri mafi kankanta a duniya da yake rike da kambun a baya, wanda shima a kasar ta Japan ne, mai nauyin gram 268, a lokacin da aka haife shi a shekarar da ta gabata. A watan Fabrairu ne aka sallami shi wancan jaririn daga Asibiti a wani Asibiti da ke birnin Tokyo, na kasar ta Japan. A lokacin da aka haifi Ryusuke, a ranar 1 ga watan Oktoba, 2018, tsawonsa shi ne Santimita 22 (kimanin inci 8.66), ma’aikatan Asibitin ne suke ajiye tare da lura da shi a wani sashe na musamman a cikin Asibitin. A lokuta da yawa sukan yi amfani da auduga ne wajen dangwalowa da ciyar da shi da nonon mahaifiyar na shi a bakinsa. Kusan watanni Bakwai da haihuwar na shi, sai nauyinsa ya ninka har kusan sau 13, a halin yanzun da za a sallame shi, nauyin na shi ya kwarari kilogram uku. a karshen makon nan ne ake sa ran sallamarsa daga Asibitin yara na garin Nagano, da ke tsakiyar kasar ta Japan. “A Lokacin da aka haife shi, kankantar na shi ta kai matuka, har ana ganin da zaran an taba jikinsa yana iya karyewa gida biyu. A lokacin na shiga cikin damuwa matuka,” in ji mahaifiyar tashi, Toshiko. “Amma a halin yanzun, ina cikin farin ciki, domin har yakan iya shan nono. Muna iya yi masa wanka ma. Ina jin dai, domin na ga yana ta kara girma a kullum,” in ji mahaifiyar.