Shugaban karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, Alhaji Abdulrahman Maigoro, ya amince da samar da rijiyar burtsatse 30 a yankin don maganin matsalar karancin ruwan sha da ake fama dasu a karamar hukumar da makwabtanta.
Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da jami’in watsa labaransa, Mista Shuaibu Mohammad, ya raba wa manema labarai a garin Keffi ranar Jumma’a.
Maigoro, ya kuma bayyana cewa, za a gina rijiya 3 a kowannne mazaba a cikin karamar hukumar gida 10 da ake dasu.