Gwamnatin Jihar Kogi ta karbi bakwancin Kwamiti Fadar Shugaban Kasa na Musamman dake ziyarce-ziyarce gani da ido, a wani mataki na sake farfado da harkokin ilmi a fadin kasarnan.
Kwamitin wanda ya sauka a Jami’ar tarayya dake birnin Lakwaja fadar gwamnatin jihar, ya samu marabta ne daga mataimakin gwamnan jihar Chief Edward Onoja, ya tabbatar da cewa gwamnatin Jihar karkashin gwamna Yahaya Bello na da tsare tsare masu Inganci don nuna jami’ar a idanun duniya.
Ya kara da cewa yanzu haka shirye-shirye sun Kankama daga gwamnatin jihar na ganin ta sauya wa jami’ar matsuguni zuwa na dindindin.
Ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tattauna muhimman abubuwa da kwamitin ya gabatar tare da gwamnan don daukar kwakkwarar mataki.
Shugaban Kwamitin wanda tsohon Jakadan Najeriya ne a kasashe da dama Ambasada Godknows Bolade Igali ya ce jami’ar ba za ta yi sako sako da kyautata huldar ta da kwamitin ba don samar da ɗa mai idanu.