Gidauniyar tallafawa harkokin ƙidaya ta majalisar dinkin duniya tare da haɗin gwiwar cibiyar kula da harkokin lafiya ta jami’ar garin Badin za su fara aikin yi wa masu lalurar yoyon fitsari aiki kyauta a birnin Yolan Jihar Adamawa.
Babbar jami’ar hukumar a Jihar Adamawa Misis Tulhungu Uziel ce ta sanar da hakan, lokacin da take zantawa da manema labarai, cewa a yau litinin za su fara aiwatar da aikin kyauta ga masu lalurar.
Tulhungu Uziel ta ce za su kammala aikin ne a ranar 30 ga wannan wata na satumba da muke ciki.