Rundunar sojin Nijeriya ta ce a mako mai zuwa za ta yaye mutum 4, 832 aikin soja, domin ganin an bunkasa tsaro a kasarnan musamman duba da ayyukan soji a fadin kasarnan.
Kwamandan Barikin Soji na Depot, wato Manjo Janaral Sani Mohammed, shi ne ya bayyana hakan a karshen makon nan a yayin rufe horas da jami’an sojin karo na 78.
A cewarsa za a gudanar da taron ne a wani mataki na karrama sojojin da suka yi nasarar kammala horaswar, inda za a shirya musu buki a ranar Asabar din 19 ga watan Oktoban 2019.