Za a yiwa shugaban kasar Czech Milos Zeman allurar rigakafin korona a cikin makon nan. Kamar yadda hukumomi a kasar suka tabbatar a ranar Lahadi.
Shugaban wanda ya ce fama da ciwon suga da wadansu cututtuka, ya tsara sai a cikin watan Fabariru zai amince a yi masa allurar. Sai dai daga baya mashawartansa sun sanya shi ya gamsu da a yi masa allurar a nan kusa. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran CTK ta tabbatar.
Zeman ya jinjinawa tarayyar Turai bisa gudummawar suka bayar wajen siyawa membobin kungiyar rigakafin.