Darektan ma’aikatar lafiya ta yammacin Afirka Mustapha Bittaye ne ya bayyan cewa, Gwamnatin Gambia na binciken ko mutuwar kananan yara sakamakon ciwon koda a yan watannin nan, na da nasaba da wani maganin Zazzabi da ake hadashi a kasar. .
BBC ta ruwaito cewa, Bincike ya nuna cewa an gano wannan matsalar na koda a tsakanin yara a kasar da ke da shekaru biyar a ƙarshen Yuli wannan shekara.
KARNATA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Chelsea Ta Tabbatar Da Graham Potter A Matsayin Sabon Kocita
Da yake jawabi Daraktan Ma’aikatar, ya bayyana cewa, yara da dama ne suka mutu a cikin watanni ukun da suka gabata, amma kuma ana tunanin cewa akwai yuwuwar wani maganin zazzabi da ake hada shi a kassr ne ya haddasa lamarin.
Sai dai har yanzu ba a bayyana ko ana binciken nau’in wani Maganin zazzabi da ake zargin ba, amma ana tsammanin guda ne daga cikin wanda ake hadawa kuma ake sayar da shi a cikin kasar ta Gambiya.
A cikin wata sanarwa da hukumomi kiwon lafiyar kasar suka fitar a makon da ya gabata, ta ce irin wannan cuta sau da yawa tana da dalilai fiye da daya.
Rahotanni sun nuna cewa cikin wata daya da ya gabata, ma’aikatar lafiya a kasar ta Gambiya ta ba da rahoton mutuwar mutane 28 amma ana fargaban adadin ya fi haka a yanzu.
A WANI LABARIN KUMA: Shugaban Karamar Hukumar Da Akayi Garkuwa Da Shi A Filato, Ya Shaki Iskar Yanci
Shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Jan Gotip, ya shaki iskar Yanci kwanaki kadan bayan yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred ne ya tabbatar wa manema labarai sakin wanda shugaban, ya kuma kara da cewa an sako Henry ba tare da jin rauni ba a daren jiya Laraba.