Sabon shugaban Hukumar yiwa Malamai Rijsita ta Nijeriya, wato TRCN, Farfesa Segun Ajiboye, ya tabbatar da cewa zai bunkasa harkar Malamai a Nijeriya.
Sabon shugaban ya bayyana hakan ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zabensa a karo na biyu domin ya sake wadansu shekaru biyar yana shugabancin hukumar.
A cikin sanarwar da Oludayo Tade, mai bashi shawara kan harkokin kafafen watsa labarai ya fitar a ranar Laraba a garin Ibadan, ya ce Farfesa Ajiboye ya karbi takardar sabunta aikin ne a hannun Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Sunday Echono.
A cewar Oludayo Tade ya ce Farfesa Ajiboye ya kuma mika jinjina da godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa sake ba shi dama da ya yi har na tsawon shekaru biyar domin ya yi aikinsa.
Ajiboye ya ce sake zabarsa yana da alaka da aikinsa bisa jajircewa da sadaukarwa, inda ya yi alkawarin sake sadaukarwa da jajircewa wajen yi wa tsarin koyarwa kwaskwarima domin ya dace da tsarin duniya.
“shugaban kasa ya sake kalubalanta ta domin na maishe da manufofina a aikace”, inji shi.
“tare da tawagata a TRCN, zamu cika alkawari a tsawon shekaru biyar din nan; zamu bunkasa walwalar Malamai tare da kawo musu fasaha a harkar koyarwa a Nijeriya”, ya tabbatar.