Gwamnatin tarayya ta yi ikirarin cewa “abubuwa da yawa suna faruwa a bayan fage” a kokarinta na warware yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako mako wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa.
ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu, kuma tun a wancan lokaci aka rufe dukkan jami’o’in gwamnati.
“Ina fata maganar ASUU ta kasance mai sauki kamar yadda yawancin mu ke tunani. Ba na tsammanin yana da sauƙi haka. Amma ina so in tabbatar muku da cewa abubuwa da yawa suna faruwa a bayan fage.
“Kuma ina ganin mai yiwuwa Ministan Ilimi zai fi dacewa ya ba da cikakkun bayanai. Amma kamar kowace gwamnati, idan ba mu damu ba, ba za mu kafa dukkan kwamitocin da ke aiki ba. Idan ba mu damu ba, ba za mu nemi hanyoyin da za mu shawo kan tunanin kungiyar ba.
“Muna cikin damuwa, mun damu, kuma za mu ci gaba da yin aiki don gano bakin zaren warware matsalar,” in ji Mohammed.