JARIDAR DIMOKURADIYYA: Ministar kudi ta Nijeriya, Hajiya Zainab Ahmad ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara nazarin hanyoyin da za ta bi wajen ganin ta daina biyan kudaden tallafin man fetur, domin samun karin kudin shiga ga gwamnati.
Hajiya Zainab ta shaida hakan ne jiya Alhamis a bayan fagen taro da asusun bada lamuni na duniya yake gudanarwa da hadin gwiwar bankin duniya, a birnin Washington na kasar Amurka.
wannan ya biyo bayan shawarar da asusun bada lamunin ya baiwa Nijeriya da sauran kasashen duniya kan Tallafin man fetur din.