Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta fara binciken wadansu kusoshin gwamnati da ake zargin sun karya ka’idojin cutar annobar korona.
Gwamnatin tarayya za ta fara bincikar shafaffu da mai din ne wadanda ke karya ka’iojin da aka shimfida a filayen sauka da tashin jiragen saman kasar domin kauce wa kamuwa da cutar Korona da nufin hukunta su in har an same su da aikata laifuka.