Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce kaddamar da dala miliyan daya na shinkafa, ya nuna cewa kasar na cigaba da samun wadatuwa a fannin samar da abinci, kuma da wannan za mu iya dogaro da kanmu wajen noman shinkafa a kasar nan ba da jimawa ba.
Shugaban kasar, a wajen kaddamar da dalar ta shinkafa a Abuja, ya shawarci kungiyoyin noma, da kada su shiga cikin shirin Anchor Borrower sai dai su yi hakan domin tallafa wa manufar wadatar abinci a kasar.
Ya yi farin ciki da hada-hadar kamfanonin shinkafa na kasar ya karu daga goma sha biyar zuwa sama da hamsin, kuma yana da tabbacin za a kara samar da ayyukan yi idan karin guda biyu a Legas da Katsina suka fara aiki.
Shugaban, ya yaba da kokarin da babban bankin kasar ke yi na farfado da kasuwar hada-hadar kayayyaki ta kasar bayan amincewarsa kuma yana fatan hakan zai haifar da samar da masu sayan amfanin gonakin noma, ta yadda za a kawar da noma zuwa kasuwar hada-hadar kudi.