Wani malamin Jami’a, Farfesa Abdulrahman Oloyede, ya ce abin da Nijeriya ke bukata domin magance matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu shi ne tattaunawa ba wai tada zaune tsaye ba.
Oloyede wanda yake Malami ne a Sashen Larabci da Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ibadan (UI), ya yi wannan bayanin ne a ranar Lahadin a wani taron karawa juna sani da Kungiyar Kungiyoyin Ahlus-Sunnah a Nijeriya (FASON) ta shirya, a Ibadan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa taron karawa juna sani mai taken: “Karya da Gaskiyar Kasar Najeriya Daya”.
Oloyede, shi ne Babban Limamin UI, ya ce daidaikun mutane da kungiyoyin da ke neman kasar al’ummar Yarbawa za su iya samun abin da suke so ba tare da an raba kasar ba.
“Duk abin da muke so a Nijeriya, za mu iya samun sa ba tare da ballewa ba.
“Bai kamata mu dauki kanmu a matsayin Kanuri ba, Hausawa ko Yarabawa, ya kamata mu dauki kanmu a matsayin ɗaya, inji shi.