Daga Sulaiman Musa
Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta kasa (ASUP) ta bayyana cewar za ta cigaba da yajin aikin da ta fara sama da kwanaki 17 har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta fara cika yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
Da ke ganawa da ‘yan jarida a shalkwatar ASUP da ke Abuja, shugaban kungiyar na kasa, Anderson Ezeibe, ya bayyana cewar akwai bukatunsu da dama da suke son gwamnati ta maida hankali a kansu kafin ta fara shirin janye wannan yajin aikin.
Ya ce, duk da bukatunsu suna da yawa ciki har da hakkokin da suke bi, suna son gwamnatin ta fara motsawa domin biyan wasu, yana mai cewa yin hakan ne kawai zai basu damar janye wannan yajin aikin da suke kai.