Sai mun kama duk wanda muka kama yana saida rago a bakin hanya, Hukumar FCTA
Hukumar FCTA dake kula da birnin Abuja ta gargadi masu sayar da Raguna inda ba nan aka kayyade ba, zata kamasu don fuskantar hukunci.
Jagoran hukumar tsaftace muhalli na Abuja, Ikharo Attah, ya gargadi Mutanen a lokacin da yakai samame a wata Kasuwar boye dake Dutse Alhaji a Abuja. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta ruwaito.
Hukumar FCTA za ta nemi a hukunta duk wanda ta kama a Kotu. Kamar yadda Attah yace.
KARANTA:- TALLAFI: Wata Kungiya ta tallafawa Yan gidan kaso a Kano
Ya bayyana hakane lokacin da ya Kai samame a kasuwar, yace duk wanda muka kama zamu kwace ragon sannan a hukunta mai ragon.
Yace ” Muna bukatar ganin masu sayar da ragunan a guri daya, sai dai su kuma basa san zama guri daya.”
“Mun basu gurare inda zasu sayar da ragunansu, su kuma masu saye za su samesu inda suke don su saya suyi bautar Allah dashi.”
“Sai dai abun mamaki sai wasu suka ware su kaje Dutse Alhaji suka bude sabuwar Kasuwar boye ta Raguna, Wanda mun kashe kasuwar tun 2019.”
Attah ya gargadi Mutanen, duk mai niyyar sayar da rago to yaje inda aka tanada don yin hakan.
Yace “akwai kasuwannin Raguna a Dei-Dei, akwai a Kugbo, sannan akwai kasuwannin Raguna a duk kwata a hade.”
“Za mu cigaba da kwace ragunan duk da mukaga ba a sayar dasu a kasuwannin da muka tsayar.”
“Idan muka kwace za mu kaima marayu da marasa karfi don su sha bikin sallah dasu.”
Mista Kaka Bello daya daga cikin mai kula da yanayin garin Abuja yayi magana kan sayar da ragunan da akeyi akan hanya.
Bello yace “Za mu turo hukumar FCTA ta cafke duk wanda ta kama yana sayar da raguna akan hanya.”
Comments 1