A wani sabon mataki na karfafa alakar Nijeriya da kasar Iran, Gwamnatin Nijeriya ta nemi zurfafa alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran yayin da Iran din ke duba yiwuwar fara jigila kai tsaye da tashin jiragen sama zuwa Najeriya.
Ministan Harkokin Waje na Nijeriya Geoffrey Onyeama ne ya yi wannan roko a ranar Alhamis a yayin wata ganawa ta hadin gwiwa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian.
Kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya rawaito cewa mutanen biyu sun yi ganawar ne a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana yanzu haka a birnin New York na Amurka.