Alhaji Ahmed Matane, Sakataren gwamnatin jihar Neja ya bayyana cewa; gwamnatin ta kammala shirye-shiryen sanya Kamarorin sirri da aka fi sani da CCTV a duk fadin jihar a wani mataki na yaki da rashi tsaro musamman na ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu satar shanu da sauran bata gari a jihar.
Matane, ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da jami’an kafafen watsa labarai, jami’an tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki a dakin taro na Legbo Kutigi a Minna.
Ya jaddada cewa; gwamnatinsu za ta yi amfani da kimiyya da fasaha wajen dakile rashin tsaro a jihar, sannan za ta yi amfani da dukkanin matakan da suka dace wajen yaki da rashin tsaro a jihar.