Za Mu Sauƙaƙa rayuwar Alƙalai a Najeriya – Shugaba Buhari
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce Gwamnatinsa za ta sassauta sharuddan da alkalai ke aiki a ƙasar.
Ya bayyana haka ne a fadar Gwamnati da ke Abuja, Alhamis, yayin da yake karbar shugaban kungiyar da wakilan kungiyar Benchers.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mutane Dubu 18,429 suka kamu da Cutar Hanta a Jahar Nasarawa
Ya ce tabarbarewar walwala da yanayin aiki na ɓangaren shari’ar kasar “na da matukar muhimmanci kuma za a kula da su yanda ya kamata”.
Buhari, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya ce Najeriya “a halin yanzu tana fama da rashin tsaro, cin hanci da rashawa da ƙalubalen tattalin arziki” wanda cutar COVID-19 da yaƙin Ukraine ya tsananta.
A cewarsa, duk Gwamnatin Dimokuraɗiyya ba za ta iya tsayawa ba inda daya daga cikin ginshikanta guda uku, wato bangaren shari’a, ba a kula da shi yadda ya kamata, da kiyayewa da kuma ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan da kundin tsarin mulki ya tanada.”
Ya kuma yi alkawarin ɗaukar matakin gaggawa kan rahoton kwamitin da ya kafa a shekarar 2018 domin duba jin daɗi da yanayin aiki na ɓangaren shari’a.
Ya taya kungiyar Benchers murnar kammala ginin rukunin gidaje Benchers da ke Jabi, inda ya amsa gayyatar kwamitin domin ƙaddamar wa.
Shugaban Ƙungiyar Benchers Wole Olanipekun, ya bayyana yanayin da Alkalai musamman alkalan kotun koli ke aiki a matsayin abin tausayi da ban tsoro.
“Muna so mu roke ka. Muna bukatar mu ba shawara kan ɓangaren shari’a. Lamarin ya yi muni. Mu tausayawa ɓangaren shari’a. Na san ka da mutunta ɓangaren shari’a. Kana da tausayi da kulawa.