Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
A daidai lokacin da a ke ganin fitaccen Darakta Aminu Saira ya kure basirar sa a wajen shirin Labarana, wanda a ke ganin babu wani fim da zai yi a nan gaba da zai kai shi, sai ga shi
Daraktan ya Sha alwashin shirya wani sabon fim din da zai wuce Labarana a nan gaba.
Daraktan ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya dangane da surutun da mutane su ke yi a kan cewar nan gaba babu wani fim da Aminu Saira zai yi wanda zai kai Labarana.
Ina da ya ke cewa
“Wannan hasashe ne kawai da mutane su ke yi Amma dai mu mun san ba haka ba ne. Domin ko a baya da muka yi fim din Ga duhu Ga haske, ai haka a ke fada, amma daga baya finafinan da suka biyo bayan sa sai kuma aka rinka fadar cewar sun fi shi kyau da tsaruwa, saboda haka don a yanzu ma an fadi haka wasu ne dai su ke ganin hakan Amma dai a wajen mu ba haka ba ne.
Ya Kara da cewar ‘Ai shi fim tsari mai inganci shi ne ya ke sa ya yi kyau don haka mu daman muna yin abin mu ne cikin tsari wannan ya sa a kullum idan muka yi aiki ya ke samun karbuwa.
Duk lokacin da za mu yi aiki sai mun dauki dogon lokaci muna tsari da kuma kasafin kudin da za mu yi, don ko a lokacin da muka shirya Labarana ai wasu kawai gani su ke yi bata lokaci mu ke yi.
Amma mu mun san abin da mu ke yi, kuma ga shi da ya fito Allah ya sa ya samu karbuwa.”
Dangane da shirin su na gaba kuwa cewa ya yi” Mutane su jira nan gaba kadan domin muna da wani shiri na gaba wanda za mu shirya fim din da ya fi na Labarana, kuma ba Wai guda daya ba, suna da yawa, amma dai a yanzu bayan Labarana akwai fim daya da muka sa a gaba wanda nan gaba kadan za mu shiga shirye shirye a kan sa kuma ina sha Allahu za mu yi aiki mai inganci daidai da zamani ”
Daga karshe ya yi kira da masu shirya fim da su rinka samar da kudi su na shirya fim mai inganci domin sai an yi fim mai kyau za a kalla kuma a yaba.