Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata ta bayyana cewa za ta tura wata tawaga mai karfi domin ganawa da Sanata Ike Ekweremadu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Idan za’a iya tunawa jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Ike Ekweremadu, wanda shine tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, an tsare shi ne tare da matarsa bisa zargin “cire sassan jiki wani yaro ” a kasar Ingila.
Majalisar ta yanke hukuncin ne bayan sun yi wata ganaawar sirri, na tsawon sa’o’i biyu a ranar Laraba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Ibrahim Lawan ne ya yabawa lauyoyin da suke kare Sanata Ekweremadu da matarsa, wadanda ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin an fitar da su daga komar rundunar yan sandan birtaniya.
Ya bayyana cewa ya gana da babban kwamishinan Biritaniya wanda ya yi masa bayani kan ci gaban shari’ar da kuma cikakken bayanin abin da ya faru.
Lawan ya kara da cewa tawagar majalisar dattawan za ta hada da mambobin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje.
“Tawagar majalisar dattawan za ta hada da mambobin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje wadanda za su yi tafiya nan da kwanaki biyu masu zuwa,” in ji Lawan.
A wani labarin kuma na daban.
Rundunar Soji zata yi amfani da Tsaffin Sojoji domin magance matsalar tsaro
Rundunar Sojin Ƙasa zata cigaba da amfani da Tsofaffin Sojoji wajen magance matsalar tsaro a ƙasar, kamar yadda Shugaban Sojojin Ƙasa Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya bayyana.
Yahaya ya bayyana haka a ranar Talata da daddare a wata liyafar cin abinci daya shirya ga Jami’an Soji da suka ajiye aiki a Shekarar 2021 daga Division na 3, Rukuba, Kusa da Jos.
Shugaban Sojin wanda ya samu wakilcin Shugaban Barikin kuma Shugaban Shirin Operation Safe Haven Manjo-Janar Ibrahim Ali, ya godema Jami’an Sojin da sadaukarwar su, da Jajircewa a lokacin da suna aiki.
Ya bayyana cewa irin ƙwarewar da tsofaffin Sojojin suka nuna ana buƙatar shi wajen cigaban Rundunar Sojin Ƙasa a kokarin ta na magance matsalolin tsaro a Kasar.
“Akwai wani yunƙuri da muke yi domin amfani da Tsaffin Sojoji dake da gogewa ta aiki, domin ya zama dole wajen magance matsalolin tsaro na Ƙasar mu,” Inji shi.
Yahaya ya ƙara dacewa,wannan liyafar cin abinci da aka shirya masu, an yi ta ne domin yabawa da irin aikin da suka yiwa Ƙasar su.
Shugaban Sojin ya yi kira ga Jami’an Soji da suke aiki a halin yanzu da suka ƙoƙari wajen tsare martaba da kima ta Ƙasa, yana mai shan alwashin baiwa jindadin su fifiko.