Cibiyar kula da ci gaban mata, NCWD ta yi alkawarin ganin ta hada hannu da ‘yan Nijeriya da kuma kasashen waje wajen ganin sun bunkasa al’amuran mata.
Daraktan Cibiyar, Mary Ekpere-Eta ce ta yi alkawarin hakan a sakon sabuwar shekara da ta fitar a Abuja.
Ta yi tilawar yadda zanga-zangar #EndSARS da kuma annobar korona da dokar kulle a 2020 ya shafi al’amuran mata da kananan yara inda ta ce duk sun gurgunta tattalin arzikin mata da sauran iyalai.
Ta ce cibiyarsu za ta ci gaba da gwagwarmayar ganin an bunkasa walwalar mata, ba su kariya ta hanyar bullo da shirin da zai amfane su ya kuma amfani marasa galihu da ‘yan gudun hijira.