Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro da su farauto ‘yan ta’adda a cikin iyakokin Najeriya, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya ce jami’an tsaro na da hurumin farauta, bibiyar su, da kuma magana da ‘yan ta’adda da yaren da suka fi fahimta.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen taron kan hadin kan yan kasa, zaman lafiya da tsaro wanda cibiyar hulda da jama’a da abokan hulda ta Najeriya ta shirya, wanda aka gudanar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsalar Tsaro: Idan Na Sauka A Mulki, Mutanen Jihar Kogi Zasu Yi Kewa Na– Gwamna Bello
Buhari wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce za a fatattaki ‘yan ta’adda daga Najeriya.
Yace, Ya yi alkawarin samun nasarar magance ta’addanci da ‘yan fashin dajj a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa: “Mun umurci sojoji da su murkushe wadanda ke addabar ‘yan kasar, sannu a hankali za’a dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
“A cikin kwanaki biyun da suka gabata, tabbas kun ji labarin adadin ‘yan ta’addan da sojoji suka kashe, da kuma adadin wadanda aka yi nasarar ceto su daga hannun garkuwa da su.
“Dole ne mu kai farmaki ga ‘yan ta’addar, mu nuna cewa babu wata maboya a cikin iyakokin kasarmu.
“Kowannen za a farauta, a bi su kuma a yi magana da su cikin harshen da suke fahimta.”
A WANI LABARIN KUMA: Horon Da Na Samu A Indiya, Ya Yi Tasiri Ga Nasarorina A Aikin Soja—- Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya ce horon da ya samu a Kwalejin Tsaro ta Indiya da ke Wellington na kasar a shekarar 1973 ya kasance wani bangare na nasarar da ya samu a aikin soja, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin karamin ministar harkokin waje da majalisar dokokin kasar Indiya, Vellamvelly Muraleedharan, a fadar gwamnati da ke Abuja.