Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya gargadi al’umma da su guji yada kalaman batanci a kafafen sada zumunta na zamani wadanda ka iya tada zaune tsaye.
Gwamna Badaru ya yi wannan jan kunne ne a yayin da gamayyar ƙungiyar masu amfanin da kafafen sada zumuntar ta kai mishi ziyarar barka da Sallah a gidan Gwamnati dake Dutse fadar gwamnatin jihar.
Ya ce kafafen sada zumunta ba wai an yi su ne su zamo wuri na watsa kalaman firgici da kawo ɗar-ɗar a tsakanin jama’a ba, a’a sai dai don hada kan jama’a, don haa dole masu amfani da shi su yi taka tsantsan.
Tun da farko da yake tsokaci, jagoran tawagar wanda kuma shine Mataimakin gwamnan jihar, Auwal Danladi Sankara ya ce babban Musababbin kai ziyarar tasu shine don taya gwamnan murnar sallah kana a lokaci guda su jinjina mishi bisa jajircewa a tsawon mulkinsa tun daga 2015.
Sankara ya ce lallai gwamna Badaru ya ci lambar yabo duba da irin yadda ya ja matasa a jika musamman masu amfani da kafar intanet wadanda da ma mafiya yawan masu amfani da shi din matasa ne.
Kazalika shugaban kungiyar a nashi ɓangare Ahmad Rufai Gumel ya yaba wa Badaru bisa ayyukan raya al’umma da ya samar a tsawon zangon mulkinsa.