Jam’iyyar APC ta ce za ta yi maraba da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan idan ya yanke shawarar shiga jam’iyyar mai mulki.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan lokacin a kafar talabijin na Channels Television jiya yau Laraba, ya ce, idan tsohon shugaban na Najeriya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar su, hakan zai karfafa tsarin jam’iyyar.
“Wannan shi ne karon farko da nafajin hakan, Amma Muna tsammanin tsohon Shugaban zai sugo jam’iyar mu kuma zai zama babban labari a gare mu. Za mu yi masa maraba; hakan kuma zai karfafa jam’iyyar, ”in ji Akpanudoedehe.
Lokacin da aka tambaye shi ko APC za ta zabi Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa idan har ya shiga cikin ta, kakakin jam’iyyar bai tabbatar ba, Kuma bai kore wannan batu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga ba su turomana da Sako ba, inji Kwalejin Tarayya dake sokoto
Inda ya ke cewa, jam’iyya mai mulki ta APC tana da rangwame na musamman ga sabbin membobi ta, gami da alfarmar yin takarar kowane mukamin siyasa a fadin kasar nan
“Majalisar zartarwar Jam’iyar APC NEC a zahiri ta ba da izini ga kowane mutum cewa, idan ya shiga APC a yau, ya zama cikakken Mamba.”
“Don haka, duk wanda ya shiga yau yana da irin wannan damar ta tsayawa takarar kowane ofishi a cikin wannan jam’iyya ”inji shi.
Jonathan ya zama shugaban Najeriya bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua a ranar 5 ga Mayu, shekarar 2010.
Tsohon Gwamnan Bayelsa, kuma Yar’Adua yayi takaran Shugaban kasa da shi a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a shekarar 2007.
Bayan lashe zaben shugaban kasa na 2011, Jonathan ya sake tsayawa takara, yayin da ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam’iyar APC a shekarar 2015.
Yayin da zaben 2023 ke kara matsowa, rahotanni na nuna cewa tsohon Shugaban na iya barin babban jam’iyar adawa ta PDP zuwa APC mai Mulki, sannan kuma yana tunanin sake yin takarar kujerar shugabancin kasar nan.
Comments 1