Za Mu Yiwa Gwamna Sule ritayar Siyasa a 2023 – PDP
Jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa ta sha alwashin tura gwamna Abdullahi Sule kasar Saudiyya a shekarar 2023.
Mista Francis Orogu, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Karu a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin da yasa Jamhuriyar Nijar ta sanya wa wata hanya sunan Shugaba Buhari – Fadar Shugaban Ƙasa
Orogu ya yi zargin cewa gwamnan ya nuna cewa ba shi da ikon gudanar da mulkin jihar inda ya yi takama da cewa PDP za ta kore shi Saudiyya a karshen wa’adinsa na farko.
Kalaman sa: “APC bisa ga dukkan alamu ta gaza wa al’ummarmu, saboda haka zabe mai zuwa na tafiya ne kawai ga PDP. Nan da 2023, za mu mayar da shi Saudiyya.”
Mista Orogu ya caccaki Gwamnan bisa zarginsa da shan alwashin murkushe duk wanda ya tsaya tsakaninsa da kujerar Gwamna gabanin zaben 2023, yana mai tabbatar da cewa PDP ba za ta ji tsoro ba.
Sai dai ya yi gargadin cewa jam’iyyar adawa za ta bijirewa duk wani tursasawa da ake zargin jam’iyya mai mulki ta yi ta hanyar da ta dace, yayin da ya bukaci al’umma da su tabbatar sun kirga kuri’u.
Tun da farko, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Dr David Ombugadu, ya yi kira ga shugabannin da su guji tayar da fitina.
Ya ce jam’iyyar PDP ba za ta gangara zuwa APC ba, yana mai cewa jam’iyyar za ta tsaya kan yadda za ta ciyar da kasar nan da jihar gaba.
A wani labarin kuma: 2023: Mafi Yawancin Yarabawa Tinubu ne zasu Zaɓa — Dattawan Yarbawa
Majalisar Dattawan Yarbawa, YCE, a jiya, ta bayyana kwarin guiwar cewa mafi yawan al’ummar Yarbawa za su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.
Da yake zantawa da ‘yan jarida a Ibadan bayan rantsar da shi, sabon shugaban kasa na YCE, Ajibade Oyekan, ya jaddada cewa yadda yawancin ‘ya’yan kungiyar ke yi ya nuna cewa za su zabi Tinubu a zaben.