Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce za a zartar da kudirin kasafin kudin shekarar 2022 a ranar 14 ga watan Disamba mai zuwa.
Ahmad Lawan, wanda ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata, ya ce hakan ne zai baiwa majalisar damar gudanar da tsarin kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba.
Ya ce yana da matukar muhimmanci majalisar dattawa ta tsaya kan jadawalin ta, idan ba haka ba za su iya shiga cikin manyan matsaloli. “Gobe (Laraba) ne za ta kasance ranar karshe na kare kasafin kudi na kananan kwamitoci na kwamitin kasafin kudi a gaban kwamitin kasafin kudin majalisar
“Kuma yana da matukar muhimmanci mu tsaya kan jadawalin mu idan ba haka ba, za mu iya fuskantar matsala mai tsanani tare da lokacinmu don yin la’akari da kasafin kudin zuwa nan da 14 ga watan na Disamba.
“Abin farin ciki ne cewa dukkan kwamitocin mu sun gama kare kasafin kudin su tare da Ma’aikatu da Hukumomi (MDAs) a matsayin samfuran wannan majalisar dattijan.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito ya kuma bayyana cewa an samu tsaiko a bangaren sauran kwamitocin, yayin da ya bukace su da su yi aiki cikin gaggawa domin cika wa’adin da aka sanya.
“Gobe (Laraba) ko mene ne, sai sun kammala kare kasafin kudin da kananan kwamitoci ke yi a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar. “Ina da tabbacin cewa kwamitocin mu za su iya bayyana gaban kwamitin kasafin kudin nan da ranar Laraba, kuma zan bukaci kwamitin kasafin kudi ya ba da kansa ga kananan kwamitocin mu,” in shi.
“Akalla, nan da zuwa karshen mako mu kammala aikin tsaron da kananan kwamitoci ke yi a gaban kwamitin kasafin kudin domin shi ma ya iya kaiwa ga aikin, ya hada mana takardun da za mu yi aiki da shi idan muka zo kashi na gaba.