A yunkurin magance Matsalar Tsaro a Nigeria, An shawarci hukumomin tsaro a Nigeria da su yi amfani da sabuwar Fasahar zamani na 5G, da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi, don magance matsalar rashin tsaro a Fadin Kasar nan, in ji Ministan Sadarwa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a jiya Talata, yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron da Hukumomin Tsaro suka shirya, mai taken; “Haɗin gwiwa: wurin yin dubi kan Hali da ake ciki: da kuma kare Ababen More Rayuwa”
Inda Pantami ya ce, : “A wani bangare na kokarinmu na tabbatar da kariya daga mahimman kadarorin kasa, muna aiki tare da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, don fito da wani Babban Umarni da zai tabbatar da cewa, Manyan Kaddarorin Kasa, musamman a bangaren Fasaha sun sami kariya ”.
Kazalika ya Kara da cewa, gwamnati ta kafa cibiyoyin gaggawa na Na’ura Mai Kwa-kwalwa guda uku, domin yakar laifukan ta’addanci a fadin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum 2 Sun Mutu, Gidaje sun Kone, Sanadiyar Fashewar Tankokin Mai a Rivers
Ya ce: “Akwai Kwamitin Shirye -shiryen da bada Agajin Gaggawa ta Na’ura Mai Kwa-kwalwa CERRT, da ke Hukumar NITDA, inda ya ce Akwai Sashin ngCERRT a Ofishin Mai Ba da Shawara kan Al’amuran Tsaro, da kuma wani wanda aka kafa a Hukumar Sadarwa ta Najeriya wanda zai kazai fara aiki a ranar Alhamis 30 ga watan Satumba shekarar 2021. ” inji shi.
Har’ila yau Pantami ya ce, don inganta bincike da ci gaba a wannan fanni, gwamnati ta kuma kafa Cibiyar Nazari kan binciken Sirri NCAIR ta kasa, domin kula da Al’amuran Tsaro.