Ministar Kuɗi, Kasafin kuɗi da tsare-tsare Zainab Ahmed ta sanar dacewa akwai yiwuwar a ƙara kuɗaɗen haraji ga kayayyakin lemu, wanda zai haifar da hauhawar farashi.
Ta bayyana haka a lokacin gabatar da bayanai akan abubuwan dake cikin ƙiyasin kasafin kuɗi na shekarar 2022 a ranar Juma’a a Abuja, inda tace za’a ƙara kayayyakin lemu haraji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen Anambra: INEC ta soke katikan zabe dubu 62,698 da suka buƙaci a sake yi masu rajista
Tace “Domin inganta kuɗaɗen da ake tattarawa na haraji, gwamnati ta maida hankali wajen masana’antu domin samun kuɗaɗen haraji.
“Ɓullo da ƙara kuɗi a ɓangaren lemun
A shekarar 2019 ta nuni cewa akwai hukunci ga masana’antu gwamnati, wanda suka kasa cimma kuɗaɗen harajin da ake tunanin samu daga wajen su.