Za’a ƙara tono man fetur a wata jihar Arewa
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya jaddada kudirin jihar Kebbi na fara samar da man fetur da kamfanin man fetur na kasa (NNPC).
Gwamnatin jihar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin mai na NNPC kan samar da man fetur a kudancin jihar shekaru biyar da suka gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsoho Ya Tayar Da Rigima a Cikin Banki Bayan An Hana Shi Cirar Kuɗi
Gwamnan a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a Ribah ya ce nan ba da dadewa ba za a fara samar da man fetur a yankin Danko-Wasagu. “Ina mai farin cikin sanar da ku cewa nan ba da jimawa ba Danko-Wasagu zai shiga kungiyar masu samar da mai a Najeriya”, in ji shi.
Ya yabawa jami’an tsaro da ’yan banga da suka jibge a yankin da ake hako man fetur bisa ga kokarin da suke yi na kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma bada tabbacin za a tura karin jami’an tsaro a yankin domin karfafa tsaro a cikin al’umma.
Gwamnan ya bukaci jama’a da su marawa APC baya kuma su zabi Tinubu/Shetima da Dokta Nasiru Idris – dan takarar gwamna na jam’iyyar – don ganin gwamnati ta dore da shirin samar da man fetur da sauran ayyukan yabawa da ta fara a sassa daban-daban na jihar.
A wani labarin kuma: Dalilin da ya sa ba zan taɓa daina goyon bayan Tinubu ba – Tsohon Gwamnan PDP
Sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta Gabas, Chimaroke Nnamani, ya dage cewa ba zai janye shawararsa na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Da yake bayyana dalilansa na goyon bayan Tinubu a matsayin sasanci da ‘yan kudancin kasar suka yi na marawa duk wani dan takaran shugaban kasa baya, da ‘yancin yin zabe da dai sauransu.